Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Tsaro Ta Civil Defence Ta Kafa Rundunar Mata Zalla Don Tsare Makarantu A Kwara

Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Kwara ta kafa wata rundunar mata zalla domin kare makarantu daga hare-hare. Kwamandan huk...


Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Kwara ta kafa wata rundunar mata zalla domin kare makarantu daga hare-hare.

Kwamandan hukumar ta NSCDC a jihar ta Kwara, Mista Makinde Ayinla, ya ce kafa wannan runduna zai taimaka wajen kare dalibai daga masu garkuwa da mutane.

“A wannan wata na Janairu za mu kaddamar da wannan runduna ta mata don magance matsalar garkuwa da dalibai.” Mista Ayinla ya fadawa manema labarai a Ilorin babban birnin jihar ta Kwara.

A cewarsa, an riga an horar da wasu daga cikinsu, saboda haka tare da iznin gwamna, za a tura su zuwa makarantu a wannan wata, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Matsalar satar dalibai a makarantu a arewacin Nijeriya ta zama ruwan dare, ko da yake, hukumomin sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen shawo kan matsalar.

‘Yan fashin daji kan kwashi dalibai bila adadin su kutsa da su cikin daji daga baya su nemi kudin fansa kafin su sake su.

Lamarin kan rutsa har da kananan yara da ba su ma mallaki hankalin kansu ba.

A mafi yawan lokuta sai an biya kudaden fansa ‘yan bindigar ke sako daliban.

No comments