Daga Umar Babagoro A wani bangare na jawabinsa a gurin taron karawa juna sani, wanda Butake Care for Women and Youth Initiative...
Daga Umar Babagoro
A wani bangare na jawabinsa a gurin taron karawa juna sani, wanda Butake Care for Women and Youth Initiative ta gabatar ranar Asabar din da ta gabata, a zauren taro na garin Dukku, jihar Gombe. Alhaji Umar Gurama, tsohon Sakataren ma'aikatar gwamnati a jihar Gombe ya bayyana takaicinsa bisa yadda wasu matasa suke sakin jiki su zauna suna jiran wani ya sama musu aiki, musamman matasan da suka kammala karatu a matakin Digiri.
Gurama ya ci gaba da cewa "a yanzu bana jin gwamnati za ta iya daukar dukkan matasan da suka kammala Digiri aiki", daga nan sai ya ci gaba da bayyana irin arzikin da Allah ya hore mana a kasar Dukku, wanda kullum wasu ne ke zuwa suna dibar wannan arziki.
Alhaji Umar Gurama ya bayyana Dako, Gini, da sauran ayyukan karfi a matsayin aikin da matashi zai iya yi domin ya samar ma kansa jari.
"Ga kasar noma Allah ya bamu, kuma ana samun alkhairi a noma amma sam hankulan matasanmu ba ya kan noma. Ga noman rani wanda shi kam mun zuba ido kullum sai dai wasu su zo su yi mu muna kallo bama yi", inji shi.
A karshe Gurama ya yi kira ga matasa da su yi amfanin da ilimi, da karfin da Allah ya ba su wajen samawa kansu aikin yi ba tare da sun koma suna tunanin wani zai sama musu aiki ba. Hakan zai taimaka wajen raya al'umma a cewarsa, "amma zaman matasa ba sana'a zai iya jawo su shiga bangar siyasa, ko shaye-shaye", ya lurantar.
No comments