Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

ISMA Ta Yi Wa Yara 240 Kaciya Kyauta A Jalingo

Daga Umar Shuaibu Bangaren kula da kiwon lafiya na Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky wand...


Daga Umar Shuaibu

Bangaren kula da kiwon lafiya na Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda aka fi sani da ISMA sun gabatar da Kaciya kyauta a garin Jalingo ta jihar Taraba. 

Wakilinmu ya labarto mana cewa; an dauki tsawon kwanaki biyar ana gabatar da wannan aiki a Markazin 'yan'uwa dake Jalingo babban birnin jihar Taraba. An kammala a jiya Laraba 5 ga watan Janairun 2022, jimillar yara 240 ne suka amfana da wannan aiki. 

Duba da mummunan yanayin da ake ciki na tattalin arziki da kuma hauhuwar farashin kayan masarufi a kasuwannin Nijeriya, iyaye da sauran 'yan'uwan yaran da aka yi wa Kaciya kyauta sun yi murna sosai da wannan aiki tare da miÆ™a godiyar su ga Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky da kuma yi musu addu'ar Allah ya kara musu lafiya. 

No comments