Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jam'iyyar APC Na Zargin Mataimakin Gwamnan Zamfara Da Amsar Belin 'Yan Chaina

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Jamiyyar APC a Jihar Zamfara na zargin mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Barista Mahadi Aliyu Gusau...


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Jamiyyar APC a Jihar Zamfara na zargin mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Barista Mahadi Aliyu Gusau da amsar Belin 'yan kasar Chaina masu hakar ma'adanai da ake a zargin suna da alaka da 'yan bindiga a Zamfara.

Sakataren yada Labarai na Jamiyyar APC na Jihar Zamfara, Yusuf Idiris Gusau ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Hedikwatar ofishin da ke Gusau.

Yusuf Idiris ya bayyana cewa, Jamiyyar PDP ta kalubalanci gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Matawalle akan matsalar tsaro bayan mataimakin gwamna Barista Mahadi Aliyu Gusau ne ya amshi belin 'yan kasar Chaina wadanda aka kama suna harkar ma'adanai kum ake zargin suna tare da 'yan Bindiga da ke kashe mutane da garkuwa da su, inji Yusuf Idris Gusau.

Yusuf Idris Gusau ya kara da cewa, Shugaban Kasa Muhammad Buhari ne ya haramta hakar ma'adanai a fadin Jihar ta Zamfara sai gashi an kama wadannan mutane suna hakar Ma'adanai saboda Mahaifin Mataimakin gwamnan Janar Ali Gusau shi ke da kashi saba'in na wuraren hakar ma'adanai da ake a Zamfara .

Kalubalantar Gwamna Matawalle akan tsaro da Jamiyyar PDP ke yi wa gwamna Matawalle kaikayi ne zai koma kan mashekiya in ji Sakataren yada Labaran.

Jam'iyyar APC ta kuma zargin mataimakin Gwamnan Barista Mahadi Aliyu da kwashe sama da naira Biliyan dari shida daga ciki asusun kudin Gwamnati. Shima Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na jihar, Farfesa Kabir Jabaka akan kwashe kudin naira miliyan dari uku da hamsin na hukumar Zakkah da wakafi a lokacin da yake shugabantar hukumar.

Yusuf Idiris Gusau, ya Kuma tabbatar da cewa, Gwamna Matawalle na iyaka kokarinsa na ganin samun nasara tsaro da ci gaban jihar duk da zagon kasa da 'yan jam'iyyar PDP ke masa.

No comments