Farfesa Kabir Jabaka Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Jamiyyar PDP a Jihar Zamfara, ta kalubalanci Gwamna Bello Matawalle akan matsalar ...
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Jamiyyar PDP a Jihar Zamfara, ta kalubalanci Gwamna Bello Matawalle akan matsalar tsaro da ya amshi sama da naira biliyan 31 a cikin shekaru biyu da rabi da ya yi na mulkin jihar kuma kwalliya ta ki biyan kudin sabulu.
Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na jihar, Farfesa Kabir Jabaka ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Gusau.
Farfesa Jabaka ya bayyana cewa, Gwamna Matawalle na watanda da kudin al'ummar jihar Zamfara ga wasu manyan ma'aikatan gidan Gwamnati da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar da mataimakinsa da kuma sauran 'yan majalisin kuwa ne wata akwai kasafi na musamman da suke samu daga lalitar asusun Gwamnatin jihar wanda haka ya sabawa doka, inji Farfesa Jabaka.
Farfesa Jabaka kuma tabbatar da cewa suna da alkaluman kudadan ake watanda da kudin jihar na kowane ofishin da kuma yadda ake kasafta su.
Jamiyyar PDP ta kalubalanci Gwamna Matawalle akan rashin ko in kula da yake ma al'ummar jihar ta Zamfara don abin ban takaici shi ne ana kashe mutane amma Mai girma Gwamna Matawalle na kasar Nijar kallon ko kuwa, inji Jabaka.
Kuma Jabaka ya kalubalanci Gwamna Matawalle akan gazawarsa na kammala aiki ko da daya ne wanda aka kammala aka kuma bude shi.
No comments