Ka Fice Mana Daga Kasa Nan Da Awa 72 -Sakon Mali Ga Jakadan Faransa


Gwamnatin soja ta Mali ta bai wa jakadan Faransa wa'adin awa 72 (kwana uku) na ya fice daga ƙasar kan wasu kalamai da Faransar ta yi game da jami'an gwamnatinta kamar yadda BBC ta labarto.

A ranar Juma'a ne Ministan Harkokin wajen Faransa Jean-Yes Drian ya ce gwamnatin Mali ta rasa abin yi yayin da ake ci gaba da sa'insa tsakaninta da ƙawayenta na Turai game da harkokin tsaro da kuma zaɓe.

"An kira jakadan Faransa kuma an sanar da shi matakin da gwamnati ta ɗauka na ya bar ƙasar cikin awa 72 sakamakon kalamai na takaici da ministan harkokin waje na Faransa ya yi a kwanan nan," a cewar gwamnatin.

An bayyana matakin ne cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.

Post a Comment

0 Comments