Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce kayan masarufi sun yi tashin gwauron-zabi a watan Disambar bara, irinsa na farko a cikin...
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce kayan masarufi sun yi tashin gwauron-zabi a watan Disambar bara, irinsa na farko a cikin wata takwas.
Hukumar ta ce tashin farashin ya zarta kashi 15.
Shugaban hukumar ta ƙididdiga Mista Simon Harry ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Ya ce abubuwan da suka fi tashi sun haÉ—a da gas na girki, da barasa, da kuÉ—in hayar gidaje, ta taba sigari da wanki da guga da kuma hayar tufafi.
Sauran abubuwan da farashinsu ya tashi sun haÉ—a da tufanin sakawa da takalma.
Shugaban na hukumar ƙididdiga ya ce an fuskanci tashin farashin ne a lokacin bukukuwan kkirsimeti da na ƙarshen shekara.
Shugaban ya ƙara da cewa gabanin tashin farahin na Disamba sai da aka yi wata takwas farashin kayan masarufi na sauka a ƙasar ta Najeriya.
Jihar Ebonyi ita ce ta fi fuskantar tashin farashin kayayyaki a jihohin ƙasar ta Najeriya, yayin da jihar Kwara kuma ta fuskanci ƙarancin tashin farashin kayayyaki.
Jihar Kogi kuma ita kuma ita ce ta fi tsadar abinci a watan na Disamba, yayin da jihar Edo kuma ta fi arahar abinci a lokacin, a cewar rahoton.
No comments