Kasashen Korea ta Kudu da Japan, sun ce Korea ta Arewa ta sake harba wani shu’umin makami mai linzami daga jirgin kasa a ranar J...
Kasashen Korea ta Kudu da Japan, sun ce Korea ta Arewa ta sake harba wani shu’umin makami mai linzami daga jirgin kasa a ranar Juma’a.
Gwajin harba makamin mai linzami dai shi ne karo na uku da kasar ke yi a makon da ya kare, bayan gwaje gwajen da ta yi a ranakun 5 da kuma 11 ga watan Janairun da muke, duk da takunkumin da ke kanta.
A cikin watan Satumban shekarar 2021 Korea ta Arewa ta soma gwajin harba makami mai linzami.
Cikin makon da ya kare Amurka ta laftawa Korea ta Arewa karin takunkumai karya tattalin arziki, bayan da ta zargi Korean da tsokanar fada da gangan.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Korea ta kudu ta gargadi makwafciyar ta ta, kan yadda ta take takunkuman da aka lafta mata, tare da yin gwaje-gwajen shu’uman makaman.
No comments