Wata kotu a Jihar Kano ta umarci jami'an tsaro da su ci gaba da tsare Mu'azu Magaji, tsohon kwamashinan ayyuka, bisa zargin ɓata s...
Wata kotu a Jihar Kano ta umarci jami'an tsaro da su ci
gaba da tsare Mu'azu Magaji, tsohon kwamashinan ayyuka, bisa zargin ɓata sunan
Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.
Mai Shari’a Aminu Gabari na kotun da ke Nomansland a
Kano ya kuma umarci a aika likitoci su duba lafiyar shahararren mai sukar
Gwamna Ganduje wanda aka fi sani da Ɗan-Sarauniya ko kuma Win Win.
Kazalika, Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 3 ga watan
Fabarairun 2022.
Ya umarci lauyoyi masu shigar da ƙara da kuma masu kare
wanda ake zargin da su kawo masa kundin shari’ar a ranar.
No comments