Babbar kotun jihar Abia ta umarci gwammnatin Nijeriya da ta biya diyyar naira miliyan dubu daya tare da neman gafara daga shugab...
Babbar kotun jihar Abia ta umarci gwammnatin Nijeriya da ta biya diyyar naira miliyan dubu daya tare da neman gafara daga shugaban haramtacciyar kungiyar aware ta Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu a kan sumamen da jami'an tsaro suka kai gidansa a watan Satumba a 2017.
Jagoran 'yan awaren, wanda kuma yake fuskantar wata shari'ar a kan cin amanar kasa da ayyukan ta'addanci a wata babbar kotun a Abuja, ya kai karar gwamnatin Najeriyar ne gaban babbar kotun ta jiharsa, Abia, da ke kudu maso gabashin kasar, a kan harin da ya ce jami'an tsaro sun kai gidansa a wancan lokacin.
Kanu wanda kotu ta bayar da belinsa ya tsere daga kasar bayan farmakin da jami'an tsaro suka kai gidan nasa, an sake kama shi a watan Yuni na 2021 a wata kasar waje aka dawo da shi Najeriya.
A yayin zaman babbar kotun ta jihar Abia a ranar Larabar nan Mai shari'a Benson Anya ya yanke hukuncin cewa gwamnatin Najeriya ta biya Kanu diyyar naira biliyan daya saboda lalata gidansa da ke garinsu Isiama Afaraukwu da aka yi, sannan kuma gwamnatin ta nemi gafara daga wurinsa.
Yayin da kotun ta Abia ke hukuncin, Nnamdi Kanun ya kuma bayyana a babbar kotun da ke yi masa shari'a a Abuja a yau inda Mai sharia'a Binta Nyako ta dage shar'ar tasa har zuwa 16 ga watan Fabrairu.
No comments