Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kotun Ƙoli Ta Ɗaure Robinho Shekara Tara A Gidan Yari

Kotu a Italiya ta kama tsohon ɗan wasan Brazil, Robinho, da laifin yi wa wata mata fyade. Kotun Ƙolin da ke birnin Rome ta amint...



Kotu a Italiya ta kama tsohon ɗan wasan Brazil, Robinho, da laifin yi wa wata mata fyade.

Kotun Ƙolin da ke birnin Rome ta aminta da hukuncin kotun ɗaukaka kara da ta yanke wa Robinho da abokansa biyar hukuncin daurin shekara tara.

A shekarar 2013 aka zargi Robinho da abokansa da cin zarafin wata yar Albania ta hanyar lalata, a lokacin da yake wasa a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan.

Amma da wahala ya sha ɗauri lura da cewa ɗan ƙwallon yana ƙasarsa kuma Brazil ba ta da yarjejeniyar mika dan kasarta don fuskantar hukunci a wata kasa.

No comments