Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ku Ƙara Haƙuri -Sakon Buhari Ga Al'ummar Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya buƙaci al'ummomin da ƴan bindiga suka yi wa kisan kiyashi a Jihar Zamfara da su ƙara haƙur...


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya buƙaci al'ummomin da ƴan bindiga suka yi wa kisan kiyashi a Jihar Zamfara da su ƙara haƙuri inda ya ce suna da yaƙinin cewa za su gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da ɗaukar mataki mai tsauri a kansu kamar yadda BBC ta ruwaito. 

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buharin ya nuna ɓacin ransa matuƙa dangane da rahoton da ya samu kan kisan gillan da aka yi inda ya ce shure-shure ne ƴan bindigan suke yi wanda bai hana su mutuwa ganin cewa suna fuskantar matsin lamba daga sojoji waɗanda aka inganta da makamai domin yaƙar ƴan bindigan.

Shugaba Buharin ya sake tabbatar da cewa ƴan bindigan na daf da zama tarihi a Najeriya inda ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba a yaƙin da suke yi da waɗannan mutanen da suka addabi jama'ar da ba su ji ba su gani ba.

Jihar Zamfara dai na ƙara fuskantar hare-hare masu tayar da hankali inda ko a cikin ƴan kwanakin nan sai da jama'ar wasu ƙauyuka da ke ƙarƙashin Ƙananan Hukumomin Anka da Bukuyyum da ke Jihar suka tabbatar da binne mutum 143 da ƴan bindiga suka kashe a hare-haren da suka kai cikin kwanaki biyu.

Sai dai a hira da BBC, gwamnan jihar Bello Matawalle ya ce mutum 36 aka kashe a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum amma zai tafi zuwa sauran wuraren domin tabbatar da cewa ko iƙirarin da ake yi na kashe sama da mutum 200 gaskiya ne.

No comments