Kungiyar 'Be The Change' Ta Ce Buhari Ya Ɓata Rawarsa Da Tsalle


BBC ta labarto cewa; wata ƙungiya mai rajin kawo sauyi a Najeriya mai suna Be The Change, ta zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da rashin zama abin misali wajen kamanta adalci da gaskiya kamar yadda ta yi alkawarin aiwatarwa idan ta samu mulki.

Kungiyar ta yi zargin gwamnatin da fifita wadansu jami`an gwamnati a kan wasu takwarorinsu suna zarcewa a kan mukamansu duk kuwa da cewa wa`adin aikinsu ya cika.

Sai dai gwamnatin ta musanta zargin.

Post a Comment

0 Comments