Daga Abubakar M Tahir Kungiyar matasa masu kishin masarautar Hadejia (HAYVA), ta gudanar da taron wayar da kan masu amfani da ka...
Daga Abubakar M Tahir
Kungiyar matasa masu kishin masarautar Hadejia (HAYVA), ta gudanar da taron wayar da kan masu amfani da kafafen sada zumunta na Zamani na karshe shekarar 2021.
Taron da ya gudana a dakin taro na UBJ Mall dake garin Hadejia, inda ya samu halartar matasa daga sassa daban-daban na masarautar.
Babban bako a wajen taron, Shugaba Murya Talaka, muma mataimakin na musamman ga Gwamnan Jihar Kebbi, Zaidu Bala Kofar Sabuwa, ya nuna matukar farin cikinsa kan halartar taron, inda ya ce ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta ne ya samu tasowa tun daga Birnin Kebbi Zuwa Hadejia, a matsayin mai tofa albarkacin bakinsa a wajen taron.
Zaidu Bala ya kara bayyana irin wahalar da suka sha a shekarun baya wajen aike sako ga manyan gidajen Rediyo na duniya, amma ya zuwa yanzu kana dakin ka zaka shiga ko'ina a fadin duniya.
Shima Tsohon Jakadan Nijeriya a ƙasar Turkiyya, Baraden Hadejia Alhaji Haruna Usman Ginsau, ya nuna farin cikinsa kan yadda matasan suke aika sakon yadda ya kamata ba tare da cin mutuncin wani ba.
Ambasada Haruna Usman, ya kara da cewa a matsayinsu na manya kuma Dattijai, suna bibiya sannan suna kallo waina da ake toyawa.
Da yake tsokaci mataimakin shugaban Kungiyar Hadejia Ina Mafita Initiate (HIMI), Dr. Hussain Shehu ya bayyana cewa a shekarar 2015, hukumar bincike ta farin kaya (DSS) ta gayyace su kan irin amfani da kafafen zumunta ta yadda ba su dace ba a yankin, amma a yanzu an samu ci gaba matuka kan wannan matsalar.
Dr. Hussaini Shehu ya shawarci matasan da su maida akalar alƙalumansu zuwa zaɓe 2023 domin samun ɗan takarar gwamna daga yankin na Jigawa ta gabas.
Da yake tsokaci Kwamishinan Shari'a na jihar Jigawa, Dr. Musa Adamu Aliyu, ya yi kira ga matasan a matsayinsu na Musulmai, da du sani komai za su rubuta su rubuta alkhairi domin girbar alkairi ranar gobe kiyama.
Da yake gabatar da jawabinsa Shugaban Kungiyar (HAYVA), Alhaji Umar Babuga Jibrin, ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne domin samar da haÉ—in kai ga matasan yankin.
Babuga ya kara da cewa yanzu haka sun sami nasarar ƙulla zumunci tsakanin matasan, wanda hakan zai rage yaɗa kalaman batanci a kafafen Zumunta.
Umar Babuga ya kuma yi ƙira ga matasan da su dage wajen wayar da kan al'ummar yankin muhimmancin katin zabe dana dan ƙasa.
A Karshe aka kira wakili Mai Martaba Sarkin Hadejia, Dan Madamin Hadejia ya gabatar da sakon na masarauta na ba sa gudunmawa ga dukkan ci gaban yankin dari bisa dari.
Bayan Rufe taro da addu'a an gudanar da liyafar cin abinci ga manyan baki da mahalarta taron.
No comments