Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Kurmancewa' Ya Sa An Ɗage Shari'ar Jagoran 'Win-win'

Tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gine-gine, Muaz Magaji "ya kurumce" bayan wani hatsari da ya rutsa da shi lokacin da ƴan ...


Tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gine-gine, Muaz Magaji "ya kurumce" bayan wani hatsari da ya rutsa da shi lokacin da ƴan sanda su ka taso shi za su kama shi a Abuja a jiya Alhamis, kamar yadda lauyansa ya shaidawa Kotun Majistare a Jihar Kano.

An cafke Magaji ne bayan da garin gujewa kamu ya ci karo da fitilar kan titi a motarsa.

Da yake baiyana gaban Alkalin Kotun, Aminu Gabari a yau Juma’a, Lauyan Magaji, Gazzali Ahmad, ya ce wanda yake karewa ya rasa ji na ɗan wani lokaci sakamakon raunin da ya samu bayan fitar da jakar iska ta yi a motarsa.

Ahmad ya ƙara da cewa wanda ake tuhumar ba zai iya sauraron tuhume-tuhumen da ake masa balle ya amsa ko akasin haka.

Don haka lauyan ya roƙi kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa domin nemar masa lafiya a asibiti.

Da yake yanke hukunci kan buƙatar lauyan, Gabari ya ba da umarnin a kai Magaji asibitin shalkwatar ‘yan sanda kuma ya ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda.

Sai Gabari ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Litinin, 31 ga watan Janairu.

No comments