Mabiya Shi'a a Afghanistan sun nemi gwamnatin Taliban ta amince da makarantar Jafari a hukumance a matsayin makarantar addin...
Mabiya Shi'a a Afghanistan sun nemi gwamnatin Taliban ta amince da makarantar Jafari a hukumance a matsayin makarantar addinin a Afghanistan ta kuma sanya duk wasu kabilu cikin tafiyarta, kamar yadda wani gidan talabijin na Channel One ya ruwaito.
Sayed Jawad Husseini wanda shi ne shugaban jam'iyyar JDP ya ce, "Amincewa da makarantar Jafari a matsayin makarantar addini da sanya mutanen Shi'a cikin tafiyar gwamnati a duka matakai su ne manyan bukatun da take da su.
Taliban ta yabi wannan matakin inda take cewa tana kokarin tafiya da duka bangarorin kabilun kasar da na addinai.
Kakakin Taliban Bilal Karimi ya ce: "Za a saurari duka bukatun kabilun kasar. Kuma an nemi duka kabilun su tattara muradansu."
No comments