Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mafi Yawan Igbo Na Son Kasancewa A Nijeriya -Ohanaeze

Kungiyar kare muradun kabilar Igbo da ke kudu maso gabashin Nijeriya, Ohanaeze Ndigbo, ta ce yawancin ‘yan kabilar ba su yarda d...


Kungiyar kare muradun kabilar Igbo da ke kudu maso gabashin Nijeriya, Ohanaeze Ndigbo, ta ce yawancin ‘yan kabilar ba su yarda da akidar aware daga kasar ba.

Shugaban kungiyar Ambassada George Obiozor, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba, ya ce, idan Nijeriya ta samu shugaban kasa dan kabilar Igbo, kasar da ‘yan kasar za su ga ainahin ma’anar Fedaraliyya ta hanyar adalci da daidaito.

A sanarwar mai taken ‘’Igbo sun shirya neman shugabancin Nijeriya a 2023’’, Obiozor ya ce al’ummar yankinsu za su fi ‘yan Arewaci da ‘yan Kudu-maso-Yamma dunkulewa daya, idan suka samu shugabancin kasar.

Ya ce ya kamata a yi hankali da wadanda suke son yin amfani da wata dabara tasu ta siyasa, da suke daukar kudu maso gabashi a matsayin abokan gaba, wanda ba haka abin yake ba a cewarsa.

Ya kara da cewa galibin ‘yan kabilar Igbo ba su yarda da ballewa daga Nijeriya ba.

No comments