Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Sauya Matsayi Kan Tsarin Zaben Jam'iyyu

Majalisar dokokin Nijeriya ta yi wa kudurin dokar zabe gyaran fuska, inda a yanzu 'yan majalisun suka ba wa jam’iyyun siyasa...


Majalisar dokokin Nijeriya ta yi wa kudurin dokar zabe gyaran fuska, inda a yanzu 'yan majalisun suka ba wa jam’iyyun siyasa damar zabar tsarin da suke so wajen fitar da ‘yan takara.

A bisa gyaran da majalisun biyu ta dattawa da kuma ta wakilai suka yi, a yanzu kudurin ya tanadi cewa kowace jam’iyya za ta iya fitar da ‘yan takararta ta hanyar zabar ‘yar tinke ko kai tsaye ko kuma ta sasanto.

A da majalisun sun zartar da cewa kowace jam’iyya za ta rika fitar da ‘yan takararta ne ta hanyar zaben ‘yar tinke kawai.

Bayan an mika wa Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanya hanu a kan kudurin domin ya zama doka sai ya ki amincewa da wannan tsari, yana bukatar su bayar da wani zabi, abin da ya sa aka maida wa hadakar majalisar kudurin inda ta sake bibiyar kudurin a yanzu tare da yin kwaskwarimar.

A yayin zaman da suka yi ne daban-daban a ranar Larabar nan, aka sake gabatar da kudurin, inda Sanata Yahaya Abdullahi ya gabatar da shi a majalisar dattawa yayin da Abubakar Fulata ya gabatar a majalisar wakilai.

No comments