Rfi ta labarto cewa ; dubun dubatar ‘yan Mali sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga sojojin kasar da suka yi juyin m...
Rfi ta labarto cewa; dubun dubatar ‘yan Mali sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga sojojin kasar da suka yi juyin mulki, gangamin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi kira da a gudanar da shi, domin adawa da tsauraran takunkuman da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata saboda jinkirta zaben farar hula.
A Bamako babban birnin kasar, dubban mutane sanye da kaya masu dauke da kalolin tutar kasar na ja da, rawaya da kore suka taro a wani babban fili, inda suka rera wakokin kishin kasa da nuna goyon bayan gwamnatin sojojin da ke karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita.
Baya ga Bamako daya daga cikin manyan biranen Mali da dubban mutanen suka amsa kiran sojojin kasar shi ne Timbuktu da ke arewacin kasar, sai kuma garuruwan Kadiolo da Bougouni da suma ke kudancin kasar.
A makon da ya gabata, shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka cimma matsayar laftawa Mali takunkunkumai, tare da rufe iyakokinsu ga kasar, a wani mataki na goyon bayan Amurka da Tarayyar Turai da Faransa da suka yi A-wadai da jinkirta zaben sabuwar gwamatin farar hula.
No comments