Manchester United ta ki sallama tayin bai wa Newcastle United aron Jesse Lingard a Janairun nan. Kungiyoyi da dama na son daukar...
Manchester United ta ki sallama tayin bai wa Newcastle United aron Jesse Lingard a Janairun nan.
Kungiyoyi da dama na son daukar Lingard, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kaka nan da yake baya buga wasanni da yawa a karkashin Ralf Rangnick.
United ba ta son bayar da aron dan kwallon, wanda take neman wadda za ta saye shi da tsoka kan yarjejeniyarsa mai shekara 29 ya karkare a Old Trafford.
Ciniki kan sayar da dan wasan tsakanin United da Tottenham da kuma West Ham ya bi ruwa, bayan da kungiyar Old Trafford ke fatan amfani da shi wajen neman gurbin cikin 'yan hudun farko a Premier League.
Newcastle wadda ke cikin 'yan kasan teburi, na son daukar dan wasan tawagar Ingila, domin ya ba ta gudunmuwar da za ta ci gaba da zama a gasar Premier a badi.
Newcastle ta amince ta sayi Lingard daga baya idan aka ba ta aro a cikin kunshin kwantiragin da ta gabatar wa United.
Shi kansa dan kwallon baya gaggawa, yana jiran karshen kakar bana, kafin ya yanke hukunci.
No comments