Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Hada Hoton Yari Da El-Zakzaky 'Yan Ci Da Addini Ne - APC

Daga Wakilinmu MADOGARA ta labarto cewa; jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta nesanta kanta da wani fosta da aka hada hoton...


Daga Wakilinmu

MADOGARA ta labarto cewa; jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta nesanta kanta da wani fosta da aka hada hoton Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da jagoran APC a jihar kuma tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari, wacce aka wayi gari a yau Laraba an manna a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara, jam'iyyar ta ce wadanda suka aikata hakan 'yan ci addini ne. 

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a wata takardar sanarwar manema labarai da suka yi wa take da 'LOKACIN ADDINANTAR DA SIYASA YA WUCE: AN SHA AL'UMMA SUN WARKE' wanda Honorabul Ibrahim Muhammad
(Danmadamin Birnin Magaji), Shugaban Ƙwamitin yada labarai ya sanyawa hannu a yau Laraba. 

Sanarwar ta ce; "An janyo hankalin dukkan magoya bayan Jam'iyyar APC ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Hon. Abdul'aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara)  kan wani hoton surƙulle dake yawo kan kafafen yanar Gizo wanda ke dauke da hoton Jagoran ɗariƙar Shi'a a Nigeria Malam Ibrahim El'Zakzaky da Jagoran siyasar APC a Zamfara, Hon. Abdul'aziz Yari Abubakar da nufin dangantashi da mazhabar Shi'a.

"Hakan ba komai bane illa yunƙuri ne na ɓatanci da yarfe da nufin dushe hasken Mai daraja Tsohon Gwamnan duba da irin kallon shi da ake yi a matsayin mafita ɗaya tilo wanda zai ceto Jam'iyyar APC a matakin Ƙasa da zaran Allah ya bashi shugabancinta a Taron ta na Ƙasa da ke ƙaratowa", inji sanarwar.

APC ta ci gaba da cewa; "Masu wannan yunƙurin wasu ƙananan ƙwari ne dake koyon siyasar 'CI DA ADDINI'  domin wajen aiwatar da wannan aiki na ɓatanci sun yi ƙoƙarin nuna wasu daga cikin Jiga-jigan gidan siyasar Mai daraja Tsohon Gwamnan su biyu a matsayin waɗanda suka ɗauki nauyin wannan aiki, sai dai kash, sai suka bar wata kafa wadda ke nuna wata fosta mai nuna alamar wasu 'yan Siyasar da ke adawa da ɗaukakar da Allah (SWT) ya yi masa a ƙarƙashin waɗannan hotunan da suke yaɗawa na ɓatanci.

"Akan haka muna amfani da wannan dama mu ƙara nanatawa al'umma cewa Mai daraja Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Honorabul Abdul'aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) Musulmi ne mabiyi Sunnar Manzon Rahama, Annabi Muhammad Rasulallahi Sallallahu Alaihi Wasallam da ba ya kokwanto ko ɓoye  aƙidarsa ta Sunnah a ko'ina kuma a kowanne lokaci, bai kuma taɓa wata alaƙa da mazhabar Shi'a ba domin shi ba 'ƊAN CI DA CETO BANE'", inji su.

"Muna baku shawara yaku ma'abota ɓatanci da ku daina ɓata lokacin ku akan irin waɗannan abubuwa, ku rungumi aƙidar aiki da gaskiya ko da al'umma za su fahimci inda kuka mayar da gaba su kuma amfana da jagorancin ku kamar yadda suke amfana da kyakkyawan Jagoranci irin na Tsohon Gwamna, Honarabul Abdul'aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara)", sanarwar ta jadadda.

"Yakamata kusani cewa 'KAN MAGE FA YA WAYE ', al'ummar mu sun gano illar siyasar Addini domin an gwada ta a cikin su, sun kuma gano iyakar zurfin ruwan! A Yanzu muna cikin lokacin Siyasar 'KAI DA HALIN KA NE!

MADOGARA ta labarto cewa; da ranar yau Laraba, Malam Shu'aib S Kaya, shugaban mabiya Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky a garin Gusau ta jihar Zamfara a sanarwar da ya sanyawa hannu, tuni ya nesanta kansu da wannan fostar, inda ya ce; "A madadin 'yan'uwa uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na garin Gusau ta jihar Zamfara, muna barranta kanmu da wani al'amari da aka tashi da shi a yau Laraba 12/1/2022. 

"A safiyar yau Laraba muka wayi gari wasu da ba mu san ko su wane ne  ba, sun bi sun mammana Hotuna (posters) din tsohon Gwamna jihar Zamfara, Abdul'aziz Abubakar Yari haɗe da hoton Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), inda a jikin hoton suka nuna cewa za su yi taron da suka kira na "Fund Raising". 

"Kamar suna kokarin nuna cewa shi tsohon Gwamnan Zamfara din na tafiyar da siyasarsa ne a karkashin Shaikh Zakzaky, tunda har da rubuta cewa "Shugabanmu Shaikh Ibraheem Zakzaky" a takardar. 

"Muna sanar da al'ummar Zamfara da al'ummar duniya baki daya cewa wannan wani abu ne da ya fi kama da makirci, domin babu wani abu makamancin hakan ta janibin Jagoranmu Sayyid Zakzaky ko ma almajiransa", suka jaddada. 

Sun kara da cewa; "Muna cewa, mai yiwuwa ko dai ya zama yarfen siyasa kawai ya haddasa wannan, ko kuma yunkurin bata sunan Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky daga wadanda suke kokarin ganin bayansa ta kowace hanya da yunkurin kawo karshen Da'awarsa.

"Ya kamata a sani, Shaikh Ibraheem Zakzaky Malamin addinin Musulunci ne, mai kiran al'umma zuwa ga yin tawaye ga tsarin zalunci da danniya da yunkurin tabbatar da tsarin addini, wanda zai shimfida adalci da daidaito a rayuwar al'umma. Don haka ba abin da ya hada shi da kwamacalar siyasar Nijeriya ta kowace fuska.

"A lokaci guda, muna hasashen cewa ganin yadda aka wayi gari tun farko har yanzu Shaikh Zakzaky ne kadai ya tsayu kyam wajen kokarin farkar da al'umma makircin makiya da suke yi na kashe mutanen yankin Zamfara da Sokoto da Katsina da sunan Mahara. Wala'alla, daga matakan da masu kashe mutane da sunan wadannan abin da suke kira 'Bandits' din akwai wannan motsin nasu.

"Don haka muna kara barranta kanmu daga koma me ye abin ya kunsa, muna kuma jan hankalin al'umma da su kiyaye, tunda akalla dama sun sanmu, sun san Jagoranmu, sun san Da'awarsa. A lokaci guda kuma muna kashedi ga masu irin wannan shirmen, a kan lallai Allah zai tona asirinsu kansa, kuma ba za mu kyale ba.

"Muna rokon Allah Ya mana maganin makiya, da masu kashe bayin Allah ba bisa hakki ba a kasar nan, da masu jibintar al'amuransu a zahiri da boye", suka karkare. 


No comments