Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Mazauna Ƙauyen Dong Na Filato Na Cikin Fargaba Bayan 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4

Mazauna ƙauyen Dong na Jihar Filato na cikin fargaba bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani wurin haƙar ma'adanai t...


Mazauna ƙauyen Dong na Jihar Filato na cikin fargaba bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani wurin haƙar ma'adanai tare da kashe mutum huɗu.

Maharan sun kutsa wurin ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ranar Asabar, inda suka harbe ma'aikatan.

Mai magana da yawun rundunar a Filato, Gabriel Ubah, ya ce sun tura ƙarin jami'an tsaro a yankin don dawo doka da oda.

"E 'yan sanda na sane da abin da ya faru," a cewarsa lokacin da aka tambaye shi game da faruwar lamarin.

"'Yan sanda sun je wurin da gaggawa. Sai dai abin baƙin ciki an kashe mutum huɗu da suka je wurin haƙar ma'adanan. An tsaurara tsaro a yankin," in ji shi.

No comments