Daga Abubakar M Taheer Shugaban masu sana'ar ridi na jihar Jigawa, Alhaji Danlami Malam Madori ya nuna bukatarsa kan samar m...
Daga Abubakar M Taheer
Shugaban masu sana'ar ridi na jihar Jigawa, Alhaji Danlami Malam Madori ya nuna bukatarsa kan samar musu da kasuwa ta zamani wanda za a rika hada-hadar ridi a jihar ta Jigawa.
Shugaban ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sana'ar ridi ta zama wata sabuwar hanyar kasuwanci wanda baki daga ƙasashen Larabawa kan tako musamman domin siya su tafi da shi domin suna amfani da shi a asibiti, magani da sauransu.
Alhaji Danlami ya kara da cewa jihohin Jigawa, Yobe, Bauchi, Taraba da Nasarawa sune jihohin da Allah ya hore musu ƙasar noma ridi mai ƙarfi wanda kusan kashi casa'in bisa dari ana kai wa kasashen Kamar Turkiyya, Oman, Saudiyya da dai sauransu.
A yanzu sana'ar Ridi tana daya daga cikin harkokin da suke kawowa kasarnan ci gaba suke rage halin ƙunci da radadi tsakanin manomansa da masu sayansa.
Ya kara da cewa yanzu haka gwamnatoci sun musu alƙawura daban-daban na zamanantar da sana'ar ta su har yanzu haƙarsu bata cimma ruwa ba.
Alhaji Danlami Malam Madori ya yi kira ga matasa musamman wanda suka kammala karatun babu aikin yi, da su dukufa wajen koyon noma da sana'a domin samun rufin asiri.
Haka kuma ya sake kira ga iyaye da rinka nunawa Æ´aÆ´ansu kananan sana'o'i Na hannu duk don samun ci gaban rayuwar su.
No comments