Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Mutum Shida Suka Samu Mummunan Rauni A Hatsarin Da Helikwafta Ya Yi A Bauchi

BBC ta labarto cewa mutum shida ne suka ji mummunan rauni a hatsarin da wani helikwafta mallakin rundunar Æ´an sandan Najeriya ya...



BBC ta labarto cewa mutum shida ne suka ji mummunan rauni a hatsarin da wani helikwafta mallakin rundunar Æ´an sandan Najeriya ya yi a Bauchi a jiya Laraba.

Gidan rediyon gwamnatin tarayya ya ruwaito Hukumar Bincike Haɗurra ta ƙasar, AIB tana tabbatar da labarain.

Sai dai a sanarwar da hukumar AIB ta fitar É—in ta ce babu wanda ya mutu a hatsarin.

Hukumar ta ce Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya NAMA ce ta sanar da ita faruwar lamarin kuma tuni an fara bincike.

Hukumar ta nemi duk wanda lamarin ya faru a kan idonsa ko ya naÉ—i wani bayani na faruwarsa da ya kai mata don taimaka wa wajen binciken da ake yi.

AIB ta kuma buƙci jama'a da ƴan jarida da su tsare sirrin waɗanda hatsarin ya rutsa da su ta hanyar dakatar da yaɗa jita-jita kan abin da ya haddasa hatsarin har sai an fitar da bayani a hukumance.

No comments