Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta ce ba za ta ci gaba da fitowa a cikin shiri mai dogon zango na Labari...
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta ce ba za ta ci gaba da fitowa a cikin shiri mai dogon zango na Labarina ba.
Nafisa Abdullahi, wacce ke fitowa a matsayin SUmayya a cikin shirin, ta baiyana hakan cikin wata wasiƙa da ta aikewa mashiryin shirin, Aminu Saira ranar Asabar.
Daily Nigerian Hausa ta ga kwafin wasiÆ™ar, inda jarumar ta ce ba za ta ci gaba da fitowa a cikin shirin ba sakamakon Æ™arancin lokacin da ta ke da shi cikin al’amuran rayuwarta.
“Na fita daga cikin shirin ne saboda yadda al’amura suka yi min yawa, da hakan na tabbatar ba zai bani damar ci gaba da fitowa a shirin ba.
“Na ji dadin kasancewa cikin shirin LABARINA kwarai da gaske, kuma na yi mua’ala mai kyau da dukkanin abokannan aiki na na cikin shirin, tun daga kan mashiryin shirin har zuwa abokan aiki.
Jarumar tace tana son ta maida hankali kan kasuwancinta dakuma kamfaninta, harma da shirin fim da takeyi na kashin kanta.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tuni dai masoya shirin Labarina su ka fitar da ran cewa Nafisa za ta ci gaba da shirin.
Sun fitar da ran ne bayan da a shirin na makon da ya gabata, an nuna wata ta samu mummunar ƙuna a jikin ta bayan da masu garkuwa da Sumayya su ka kunnawa sansanin da su ke riƙe da ita wuta bayan da jami'an tsaro su ka kai musu bara.
Bayan nan ne sai a ka nuno wata mace a kan gadon asibiti da bandeji a gaba ɗaya fuskar ta, hannun ta da ƙafafuwan ta, inda da dama su ke ganin Sumayya (Nafisa) ce kuma da ga nan za a canja mata fuska, wato za a sako wata jarumar ta maye gurbin ta.
No comments