Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya ce ya kashe naira miliyan dubu dari daya wajen gyara matatun man kasar a 2021 Rahoton shekara ta 2021 n...
Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya ce ya kashe naira miliyan dubu dari daya wajen gyara matatun man kasar a 2021
Rahoton shekara ta 2021 na aikin kamfanin ne ya bayyana haka ga taron kwamitin rabon arzikin kasa a baya-bayan nan.
Majalisar zartarwa ta kasar ta amince da gyaran matatar mai ta Patakwal da ke jihar Rivers a kan dala biliyan daya da rabi.
Majalisar ta amince da kudin ne a taronta na karo 38,wanda ta yi ta bidiyo karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, a Abuja.
Shugaban kamfanin na NNPC, Alhaji Mele Kyari, ya ce an rufe matatun man kasar saboda ba za a iya gudanar da su ba.
Ya kara da cewa idan za a gudanar da matatun mai na Kaduna da Warri ana bukatar a samar da gangar mai 170,000 a duk rana, a aikinsu na kashi 70 cikin dari ke nan.
Matatun mai na Patakwal da Kaduna da Warri, wadanda ke karkashin NNPC, an gina su a kan su samar da gangar mai 445,000 a duk rana.
-BBC
No comments