Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rasha Ta Kaddamar Da Sabbin Atisayen Soji A Kudancin Crimea

Rundunar sojin Rasha ta ce ta kaddamar da atisayen soji da ya kunshi dakaru kusan 6,000 da jiragen yaki akalla 60 a Kudancin Ras...


Rundunar sojin Rasha ta ce ta kaddamar da atisayen soji da ya kunshi dakaru kusan 6,000 da jiragen yaki akalla 60 a Kudancin Rasha kusa da Ukraine da kuma yankin Crimea da Moscow ta mamaye, yayin da Ukraine ta sanar da bankado wani gungu da ke samun goyon bayan Moscow ta na shirya kai mata hare-hare.

Rundunar soji a kudancin Rasha ta sanar da atisayen a matsayin wani Shirin ko ta kwana dai-dai lokacin da takun saka tsakanin mahukunta Moscow da kasashen Yamma ke kara tsanata dangane da Crimea.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce, atisaye ya kunshi ayyukan soji da dama da suka hada bada kariya da kuma maida martani a duk lokacin da abokan gaba suka ce kule.

Wannan na zuwa ne adai-dai lokacin da Ukrain ta sanar da cewa ta tarwatse shirin wasu mutane dake samun goyon bayan Rasha dake Shirin kai hare-hare wasu wurare cikin kasar wajen amfani da abubuwa masu fashewa.

Kyiv da kasashen Yamma na zargin Rasha da jibge dubban dakarunta a kan iyakar kasar Ukraine a shirye-shiryen kai hari tare da neman wargaza kasar.

Yanzu haka kasashen Yamma da Amurka na Shirin kakabawa Rasha tsauran takunkumai muddun kasar Rasha da ci gaba da Shirin mamaye Ukraine kamar yadda RFI ta labarto. 

No comments