Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rundunar Ƴan Sanda Ta Ceto Ɗaliban Islamiyya 21 A Jihar Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta ceto daliban Islamiyya 21 da wasu ‘yan bindiga suka yi ...


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta ceto daliban Islamiyya 21 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Gusau-Tsafe-Funtuwa a ranar 31 ga Disamba, 2021.

Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu, ya ce yaran sun hada da maza 19 da mata biyu. Sai dai ya ce har yanzu ba a ceto Malaminsu, Lawali Ibrahim, wanda shi ma aka yi garkuwa da shi.

Shehu ya ce, "yaran da aka yi garkuwa da su 21 da suka hada da mata biyu na daga cikin mutanen da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka sace a kauyen Kucheri da ke kan hanyar Gusau zuwa Funtua a ranar 31 ga Disamba, 2021 da misalin karfe 2300."

Ya ce, “A ranar 31 ga Disamba, 2021 da misalin karfe 2300 na safe, an samu kiran gaggawa daga kauyen Kucheri ta karamar hukumar Tsafe, inda wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtuwa da ke Kucheri, suka kuma yi awon gaba da wasu matafiya a cikin motoci daban-daban".

"Jami'an tsaro na 'yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji sun amsa kiran gaggawa kuma suka koma wurin, inda suka yi artabu da 'yan bindiga sun yi nasarar ceto yara 21 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata biyu da suka fito daga kauyen Rini da ke karamar hukumar Bakura zuwa jihar Katsina domin zuwa makarantar Almajiri Islamiyya tare da malaminsu mai suna Lawali Ibrahim.”

No comments