Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Buhari Ya Fasa Zuwa Zamfara Saboda 'Hazo'

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke ziyararsa zuwa jihar Zamfara sakamakon rashin kyawun yanayi da ya jawo hazo. Daya daga cikin ma...


Shugaba Muhammadu Buhari ya soke ziyararsa zuwa jihar Zamfara sakamakon rashin kyawun yanayi da ya jawo hazo.

Daya daga cikin masu taimaka masa a shafukan sada zumunta Buhari Sallau ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook.

Tun da fari an tsara cewa shugaban zai bi helikwafta ne daga Sokoto inda ya fara ziyarta zuwa Gusau.

Sanarwar ta ambato gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce: "Shugaban ƙsa ya yi magana da ni ya kuma umarce ni da na bai wa al'ummar jihar Zamfara haƙurikan wannan sauyi da aka samu.

"Shugaban ƙsa ya ce ya sauya ranar ziyarar tasa zuwa mako mai zuwa kuma za a sanar mana da sabuwar ranar ziyarar nan gaba kaɗan.

Gwamna Matawalle ya kuma ce: "Wasu manyan shugabannin tsaro a yanzu haka suna Katsina amma ba za su iya zuwa Zamfara ba saboda rashin kyawun yanayi

"Muna miƙa godiyarmu ga shugaban ƙsa saboda ƙaunar da yake nuna wa jiharmu," in ji Matawalle.

A yau ne Shugaba Buhari ya fara sauka a Sokoto inda ya ƙaddamar da sabon kamfanin siminti na BUA.

No comments