Daga Aisha Suleman, Zariya Kungiyar masu noman albasa da ake kira 'National Onion Producers Processors and Maketers Associat...
Daga Aisha Suleman, Zariya
Kungiyar masu noman albasa da ake kira 'National Onion Producers Processors and Maketers Association of Nigeria (NOPPMAN)' ta yi taron karawa juna sani a Zariya ta jihar Kaduna.
Wakiliyarmu ta samu halartar wannan taro ga tsarabar da ta kawo ma masu karatu.
Taron an gudanar da shi ne a babban dakin taro na Faisalco dake Kauran Juli a karamar hukumar Zariya.
Bayan manyan baki sun gama isowa ne aka bude taro da addu'a.
Sannan shugaban kungiyar masu harkar albasa na jihar Kaduna, Alhaji Sani Isma'il Kargi ya yi jawabi mai tsawo akan kalubalen da yankin Arewa ke cikin a bangare noman Albasa, inda ya ce, abin kunya ne a ce ya zuwa yanzu babu wani kamfani da ake sarrafa Albasa a yankin Arewacin Nijeriya, inda ya kira hakan a matsayin koma baya.
Shugaban ya kara da cewa yanzu haka wasu kasashen Albasan Nijeriya suke amfani da shi a matsayin ta su kasar kuma riga suke canza mata kawai su sayar da kudi mai yawan gaske.
Ya ce yanzu haka a Jamhuriyyar Nijar suna da kamfanoni da suke sarrafa Albasa fanni daban-daban ya ce haka ma kasar Ghana suma akwai ci gaba sosai; "amma duk da Albasan da suke siya a wajenmu wanda muma kamata ya yi mu tsaya mu amfana da hakan ba wasu ba", inji shi.
Ya ce; "yanzu haka Albasan da ake bukata a wajenmu ta kai akalla tan 2850. Mu kuma tan 1500 muke nomawa to ina zamu samu sauran don Allah?" Ya tambaya.
A don haka ne shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su bai wa manoma Albasa tallafi na kayan aiki da kudi da dukkan sauran abubuwan da za su karfafa noman Albasa a kasa baki daya.
Shugaban ya ce hakan zai taimaka a bangarori da dama ciki harda hanyar samun kudin shiga ga gwamnatoci.
Karshe shugaban ya kawo mafitar da aka samu a tarukansu na kasa baki daya, inda ya ce da ikon Allah dukkan mai hulda da Albasa a wannan lokaci zai dara tare da yin farinciki mai dorewa bisa kyakkyawar tsari da kungiyar ta fito da shi na tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin tafiyar.
Itama Hajiya Hauwa Ibrahim wacce ita ce shugaban mata masu Harkar Albasa ta jihar Kaduna ta nuna jin dadinta bisa yadda jama'a suka amsa gayyatar kungiyar ta su a dukkan fadin kananan hukumomin jihar Kaduna.
Shugabar na mata ta yi kira ga mata cewa su fito a dama da su domin akwai rufin asiri cikin lamarin. Kuma ta tabbatar da cewa da ikon Allah manoman albasa na fadin jihar Kaduna da kasa baki daya za su dara bisa tsari da za su kawo mai inganci.
Karshe ta yi fatan yadda kowa yazo lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya.
Farfesa Abdullahi Danladi daga Jami'ar ABU Zariya shi ko a nasa jawabin ya bayar da shawara ne ga 'ya'yan kungiyar da su riki gaskiya da rikon amana a tafiyar ta su inda ya ce hakan zai sa a sami da mai ido.
Karshe ya yi fatan alheri ga kungiyar a fadin kasa baki daya.
Shima shugaban kungiyar na karamar hukumar Zariya, Alhaji Mustafa Balarabe shi ko kira ya yi ga sabbin 'ya'yan kungiyar da kuma tsofaffi da su goyawa kungiyar baya tare da hakuri da juna, indq ya ce hakan zai taimaka wajen samun nasara a tafiyar ta su.
Sarkin Noman Lardin Zazzau ya yi tsokaci ne akan sanin yadda ake shuka Albasa ya ce wajibi ne mutum ya nemi iri mai kyau da wajen shuka mai kyau kafin gudanar da komi kuma ya yi alkawarin za su baiwa 'ya"yan kungiyar shawarwari masu inganci tare da kira ga gwamnati da ta taimakawa manoman Albasa a kasa baki daya, inda ya ce hakan zai taimaka matuka.
Taron ya sami halartar manyan baki daga bangaren Malaman Jami'a, 'yan siyasa da manyan manoma da ma'aikatan gwamnati da kungiyoyin manoma ciki da wajen jihar.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments