Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tattalin Arzikin Nijeriya Zai Haɓɓaka Da Kashi 2.5 A 2022- Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi hasashen samun habakar tattalin arzikin Najeriya da akalla kashi 2.5 cikin dari a shekarar 2022 fiye da kash...


Bankin Duniya ya yi hasashen samun habakar tattalin arzikin Najeriya da akalla kashi 2.5 cikin dari a shekarar 2022 fiye da kashi 2.4 da bankin ya yi hasashe a 2021.

Alkaluman da bankin ya fitar kan hasashen tattalin arzikin kasashe ya ce tattalin arzikin Najeriyar zai rika habaka shekara bayan shekara wanda ke da nasaba da tashin farashin man fetur da kuma kudaden da kasar ke samu a bangaren sadarwa da hukumomin kudi.

Najeriyar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika wadda kuma ta dogara da man fetur wajen samun kudaden shiga alkaluman da Bankin na Duniya ya fitar ya nuna cewa bayan samun karuwar tattalin arziki da kashi 2.5 a 2022 zai sake karuwa da kashi 2.8 a 2023.

Wasu daga cikin dalilan da za su taimakawa tattalin arzikin na Najeriya a cewar bankin akwai matakin kungiyar OPEC na rage yawan man da manyan kasashe masu arzikin man fetur ke fitarwa da kuma wasu sabbin tsare-tsare da za su taimakawa kananun kasashen kungiyar.

Sai dai duk da habakar tattalin arzikin kamar yadda bayanan bankin suka nuna, Najeriyar za ta ci gaba da fuskantar matsalolin da annobar covid-19 ta haddasawa bangaren samar da ayyukan yi.

Alkaluman bankin sun ce yanayin samar da ayyukan yi zai ci gaba da tafiyar hawainiya a sassan Najeriyar haka zalika zai dauki lokaci gabanin daidaituwar farashin kayaki musamman na abinci.

Alkaluman bankin sun nuna cewa duk da habakar tattalin arzikin har zuwa 2023 al’amura baza su koma kamar yadda su ke kafin coronavirus ba.

No comments