Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tinubu Zai Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa A 2023, In ji Kofa

Shugaban Hukumar kula da Harkokin Gidaje ta Tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa Jagoran Jami'yar APC na Ƙasa, Bo...


Shugaban Hukumar kula da Harkokin Gidaje ta Tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa Jagoran Jami'yar APC na Ƙasa, Bola Tinubu zai tsaya takarar shugaban ƙasa a kakar zaɓe ta 2023.

An daɗe a na raɗe-raɗin cewa Tinubu zai tsaya takarar shugaban ƙasa, in da shi kuma ya sha musanya hakan.

Amma, a wani taron yin addu'a ga zaman lafiyar ƙasa da kuma takarar Tinubu da Koda ya shirya a yau Asabar, a gidansa da ke garin Kofa a Ƙaramar Hukumar Bebeji a Jihar Kano, ya ce ya tattauna da Tinubu cewa zai tsaya takara.

A cewar Kofa, duk da cewa akwai ingantattun ƴan takara a APC, amma Tinubu ya fi kowa dacewa da ta riƙe ƙasar nan duba da gogewar sa a gani daban-daban na rayuwa.

"Tinubu ya san siyasar ƙasar nan. Ya san yadda zai sarrafa tattalin arziƙin ƙasa. Ya na da gogewa a fannoni daban-daban. Ya san manyan mutane a ko ina faɗin duniyar nan.

"Sabo da haka ina shaida muku cewa Tinubu zai tsaya takarar shugaban ƙasa. Ni mun tattauna da shi kuma ya tabbatar min da haka," in ji Kofa.

Kofa ya ce a yanzu haka shine Darakta-Janar na Ƙungiyar Goyon Bayan Takarar Tinubu na Ƙasa, in da ya ce yanzu lokaci kawai a ke jira a sanya ranar da Tinubu da kan sa zai furta takarar ta sa.

Tsohon ɗan majalisar taraiyar ya ƙara da cewa yana da tabbacin Tinubu zai tsaya takara har ma ya lashe zaɓen fidda gwani na APC da ma zaɓen ƙasar gaba ɗaya.

Bayan ya baiyana haka, Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kofa din ya raba tallafi Ga matasa 2,500 sannan kuma ya raba tallafi karatu ga ɗalibai 2,500 a yankin Ƙananan Hukumomin Ƙiru da Bebeji.

No comments