Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsofin Daliban Makarantar Sambo Sun Yi Bikin Cika Shekaru 40 Da Kammalawa

Daga Abubakar M Tahir Tsofaffin daliban makarantar Firamare Sambo, wanda take Haɗaka tsakanin Daliban Ƙofar Arewa da Abdulkadir,...


Daga Abubakar M Tahir

Tsofaffin daliban makarantar Firamare Sambo, wanda take Haɗaka tsakanin Daliban Ƙofar Arewa da Abdulkadir, sun gudanar da bikin cika shekaru arba'in (40) da kammala makarantar.

Taron wanda kungiyar mai suna (SAMPOPA-81) ta gudana a harabar makaranta ya samu halartar Æ´an kungiyar maza da mata.

Bayan bude taro da addu'a, an gayyaci shugaban Kungiyar Malam Gimba Bello, wanda ya yi jawabin maraba ga mahalarta taron.

Malam Gimba ya bayyana farin cikinsa kan wannan muhimmiyar rana ganin yadda wasu tun bayan kammala makarantar ba a sake haduwa ba sai a wannan lokacin.

Shima a nasa jawabin, É—aya daga cikin Æ´an kungiyar ta (SAMPOPA-81) Malam Muhammad Danladi, ya kawo hadisan Manzon Allah (S.A.W) da suke magana akan muhimmancin zumunci. Haka kuma Muhammad Danladi ya yi dogon bayani akan muhimmancin lokaci ga rayuwar É—an Adam.

Shima a nasa jawabin, Malam Yusuf Aruth, ya yi tariyar baya ga irin nasarorin da suka samu a wannan tafiya. Haka kuma Aruth ya yi abu mai ratsa zuciya na fadin sunayen malaman su da É—aliban da suka rasu, wanda hakan yasa muhallin taron ya cika da jimami.

Daga nan an gabatar da ƙyautar karramawa ta musamman ga malaman makaranta, wanda suke a raye da wanda suka rasu aka maiƙa ƙyautar ga iyalansu.

Daliban sun gudanar da karramawa ta musamman ga hukumar makarantar na bada tallafin kayan koyo da koyarwa.

Sannan kuma an karrama É—aya daga cikin Æ´an kungiyar, wanda ya samu matsayin zama Farfesa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, Farfesa Yusuf Hussaini Wakili.

Da yake jawabin godiya, Farfesa Wakili ya nuna jin dadinsa akan wannan karramawa da aka yi masa, inda ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga ƙoƙarin da Malamansu, Iyaye da al'umma gaba daya suka yi, kuma wannan nasara ta kowa ce gaba daya.

Da yake tsokaci, tsohon Hedimasta na makarantar, Malam Umar Abdullahi Dan Malam ya yi kira ga gwamnatin kan daukan tsauraran matakai kan malaman da suke sakaci da aikinsu maimakon su koyar sai su koma cutarwa.

A nasa tsokaci kan ƙyautar da aka bai wa Farfesa, Dr. Hussaini Shehu, ya jero irin wahalar da ake fuskanta kafin zama Farfesa, wanda wasu sukan ci gaba da bincike wasu kuma sukan bata a rububi.

Shima a nasa jawabin, Sakataren ilimi na karamar hukumar Hadejia, Alhaji Musa Garba ya roki alfarmar Æ´an kungiyar da su tallafawa makarantar wajen kewayenta.

A karshe Dan Malikin Hadejia Alhaji Sambo Usman ya musu nasiha kan muhimmantar da hadin kan juna ya kuma yi musu addu'ar fatan alkairi.

Da take jawabin godiya Malama Talatu Salisu, ta godewa kowa ta kuma yi addu'ar fatan alkairi a tsakaninsu.

An gudanar da hotunan tarihi na Æ´an kungiyar da malamansu.

Haka kuma tun da farko daliban sun gabatar da sunayensu da suke amfani da su a makarantar, wannan tasa suka rinƙa barkwanci tsakaninsu.

No comments