Tsohon Shugaban Nijeriya Cif Ernest Shonekan wanda ya jagoranci shugabancin kasar bayan mulkin Soji na Janar Ibrahim Babangida ya rasu.
Shonekan ya rasu ne a Legas yana da shekaru 85.
Ya kasance ya gaji shugabancin Nijeriya a tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993 kafin Marigayi Janar Sani Abacha ya yi masa juyin mulki.
0 Comments