Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Tun Bayan Kwace Gwamnati A Karon Farko Taliban Ta Amince Da Kasafin Kudinta

Kungiyar Taliban ta amince da kasafin kudinta na farko domin tafiyar da ayyukan gwamnatin ta a Afghanistan tun bayan da suka kom...


Kungiyar Taliban ta amince da kasafin kudinta na farko domin tafiyar da ayyukan gwamnatin ta a Afghanistan tun bayan da suka koma kan karagar mulki a cikin watan Agusta.

Shugabannin na Taliban sun sanar da kasafin na su ne ba tare da ambaton taimakon kasashen waje ba, wanda ta ce yawan kasafin ya kai dalar Amurka miliyan 508.

Taimakon kasa da kasa da Afghanistan ke samu a lokacin da Amurka ke marawa tsohuwar gwamnatin kasar baya, ya kai kashi 80 cikin 100 na kasafin kudinta.

Kakakin ma'aikatar kudin gwamnatin kungiyar Taliban Ahmad Wali Haqmal, ya ce a karon farko cikin shekaru 20, sun yi kasafin kudin da bai dogara da taimakon kasashen waje ba, abin da ya bayyana a matsayin babbar nasara ga kasar.

No comments