Bumburutu ita ce sana'ar sayar da mai, galibi a jarkoki a bakin titi. E, ita yarinyar wannan sana'ar na ga tana yi, duk ...
Bumburutu ita ce sana'ar sayar da mai, galibi a jarkoki a bakin titi. E, ita yarinyar wannan sana'ar na ga tana yi, duk da cewa sana'ar galibi ta maza ce.
Abin da ya faru shi ne, na dan je wani kewaye bayan gari. Bayan na kammala abin da ya kai ni, sai na yo shirin gida. Ina baro wurin da jama'a suke, sai na ji mashin ya yi buuuuu ya mace. Na ce a raina, to fa! Yanzu ya za a yi, gani a cikin kuryar wannan unguwa.
Ina daga kai sai na hango wani mutum. Sai na tambaye shi, don Allah Malam zan iya samun fetur a nan kusa? Kawai sai na ga ya nuna min wani gida kamar mita 200 daga inda nake. Na yi mamaki, kawai na tunkari gidan. Ina zuwa na tura wani yaro, na ce a ba ni kwata, da zummar ya fitar da ni titi. Ai kawai sai ga wata yarinya ta fito da fetur a hannu.
Ga alama babarta ce take siyar da fetur din, amma dai yarinya ta iya komai na masu bumburutu. Na yi mamaki sosai. Bayan ta gama zuba min fetur din a mashin, sai nake tambayar ta, wai ke gidan nan naku ba a kunna wuta ne? Sai yarinyar ta ce, "ana kunnawa mana". Na yi mamaki sosai. Sai na ce to amma ba kwa tsoro. Yarinyar ta ce "ai fetur din yana cikin uwardaki ne".
Na yi mamakin wannan babban gangancin. Duk da cewa na fahimci suna cikin kunci sosai, amma ban san me ya sa suka zabi wannan sana'ar mai cike da hatsari ba.
Allah Ya azurta mu baki daya, amin.
-Daga Muhammad Sulaiman Abdullahi
No comments