Rahotanni na cewa sojojin da ke adawa da gwamnati a Burkina Faso sun tabbatar da karbe iko da kasar bayan tsare Shugaban Ƙasar R...
Rahotanni na cewa sojojin da ke adawa da gwamnati a Burkina Faso sun tabbatar da karbe iko da kasar bayan tsare Shugaban Ƙasar Roch Kabore.
Wani soja a gidan talabijin na kasa ya bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Kabore tare da rusa majalisa.
Rahotanni sun ce sojojin sun kuma kulle iyakokin kasar. Sanarwar da sojojin suka fitar na dauke da sa hannun kanar Henri Sandaogo Damiba, wanda ake ganin shi ne ya jagoranci juyin mulkin.
Jam'iyar MPP ta Mr Kabore ta ce an yi yunkurin kasha shugaban kasar da wasu ministocinsa.
Gwamnatin Roch Kabore ta sha fuskantar suka kan gazawa wurin dakile hare-haren kungiyoyin tada kayar baya.
Tun da farko wasu dakarun ƙasar ta Afirka ta Yamma sun nemi a kori wasu manyan jami'an soja da kuma samar da ƙarin kayan aiki don yaƙar masu iƙirarin jihadi.
An jiyo harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma wasu barikin soja ranar Lahadi da dare a Ouagadougou babban birnin ƙasar.
A baya sojojin sun musanta labarin yunƙurin juyin mulki ko kuma cewa an kama shugaban ƙasar, amma kuma a yanzu kusan ta tabbata cewa sun yi juyin mulkin .
Rahotanni na cewa ana tsare da Shugaba Kabore ne a wani sansanin soja.
Kazalika, sojoji sun kewaye gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.
Ɗaruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin duk da dokar hana fita da aka saka, sannan suka dinga ƙona ofisoshin jam'iyya mai mulki.
Bidiyon da aka rika yadawa a babban birnin kasar ya nuna wasu motoci masu sulke - wadanda rahotanni suka ce na fadar shugaban kasa ne - a kan tituna.
Wakilin BBC Simon Gongo da ke Ouagadougou ya ce birnin ya yi tsit. Sai dai sojoji sun kewaye gidan talabijin na kasar.
A ranar Lahadi Ministan Tsaro Janar Barthelemy Simpore ya musanta batun tsare shugaban ƙasar da kuma yadda hatsaniyar ke faruwa.
Gidan talabijin ɗin ƙasar kuma ya bayyana harbe-harben da aka ji da cewa wasu tsirarin sojoji ne maimakon babban rikici ko kuma juyin mulki.
Yayin da layukan intanet ba sa aiki yadda ya kamata, har zuwa safiyar Litinin ana zaune cikin ɗar-ɗar a babban birnin ƙasar, sakamakon babu wani bayani daga gwamnati ko kuma sojoji.
No comments