Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Bindga Sun Hallaka Mutane Da Dama A Karamar Hukumar Shiroro Ta Jihar Neja

‘Yan bindiga sun kai hari a wani yankin karamar hukumar Shiroro da ke jihar neja, inda ‘yan sanda suka tabbatar da mutuwar akall...


‘Yan bindiga sun kai hari a wani yankin karamar hukumar Shiroro da ke jihar neja, inda ‘yan sanda suka tabbatar da mutuwar akalla mutane 13.

Kakakin ‘yan sanda a jihar ta Neja Wasiu Abiodun ne ya ba da alkaluman, tare da yin watsi da rahotannin cewar mutane 37 aka kashe a farmakin, ya kuma kara da cewar tuni aka tura jami’an tsaro domin kai daukin gaggawa zuwa yankin.

Rundunar ‘yan sandan ta ce maharan sun far wa mutanen kauyen da ke tsaka da aikin girbin amfanin gona a kauyen Nakundna a karamar hukumar ta Shiroro, yayin da kuma a cikin sanarwar da gwamna Abubakar Bello ya fitar ta nuna cewa harin ya bazu zuwa wani kauye mai suna Wurukuchi.

Alkaluman da jami’ai a jihar Neja suka fitar, sun nuna cewae sama da mutane dubu 151 da 380 galibinsu manoma suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga a cikin shekaru biyu da suka gabata.

No comments