Wasu 'yan bindiga sun yi kutse a wajen wani taron shugabannin jam'iyyar APC a karamar hukumar Enugu ta kudu inda suka bude musu wu...
Wasu 'yan bindiga sun yi kutse a wajen wani taron shugabannin jam'iyyar APC a karamar hukumar Enugu ta kudu inda suka bude musu wuta a ranar Talata.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar kusan bakwai sun kashe mutum biyu suka raunata wasu da dama yayin da suka yi awon gaba da mutum daya daga cikin shugabannin na APC na mazaba ta uku ta unguwar Obeagu Awkunanaw a karamar hukumar ta Enugu ta kudu.
Daya daga cikin wadanda 'yan bindigar suka kashe shi ne, tsohon shugaban jam'iyyar na karamar hukumar na baya-bayan nan, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban matasa na jan'iyyar na jihar a yanzu, Mista Kelvin Ezeoha.
Rahotanni sun ce ba a san ko harin na da nasaba da siyasa ba ko kuma hari ne na haramtacciyar kungiyar 'yan aware ta Biyafara ba, IPOB, wadanda suke kai hare-hare a kan jama'a a yankin kudu maso gabas na Najeriya da sunan tabbatar da dokar zama a gida.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto rundunar 'yan sanda ta jihar ta Enugu ba ta ce komai ba ko fitar da wata sanarwa dangane da harin.
No comments