Rahotanni daga jihar Kebbi sun ce, mutane da dama sun rasa rayukansu, ciki har da wasu 13 da aka banka wa wuta a cikin wani gida...
Rahotanni daga jihar Kebbi sun ce, mutane da dama sun rasa rayukansu, ciki har da wasu 13 da aka banka wa wuta a cikin wani gida, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a wani gari a karamar hukumar Riba ta jihar Kebbi a ranar Juma’a.
Wasu da suka sha da kyar sun shaida wa sashin Hausa na RFI cewa lamarin ya auku ne bayan wata arangama tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga da suka kai farmaki a garin Dankade.
Wata majiya ta ce bayan arangamar ce ‘yan bindigar suka huce fushinsu kan al’ummar yankin da suka bazama daji saboda firgici, inda suka kashe mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Wadanda suka yi hijira zuwa garin Onashi sun ce yanzu haka akwai gawarwakin ‘yan uwansu da ke kwance a dazuka, kuma babu halin zuwa dauko su saboda fargabar abin da ka iya faruwa.
No comments