'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama Tare Da Kona Gidaje A Neja


Rahotanni daga jihar Neja na nuni da cewa 'yan bindiga sun kashe mutane da dama a kauyukan Galadima-Kogo da Galkogo dake karamar hukumar Shiroro.

Jaridar Daily Trust ta ce 'yan bindigar sun kuma kona gidaje abin da ya tilastawa mazauna kauyukan Kushi da Sabon Kabula da Dangunu da Zazzaga da kuma Chibani tserewa daga gidajen su.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya Emmanuel Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Post a Comment

0 Comments