'Yan bingidar da ake zargi makiyaya ne sun kai hari ranar Lahadi a yankin Okeluse da ke Ƙaramar Hukumar Ose ta Jihar Ondo. J...
'Yan bingidar da ake zargi makiyaya ne sun kai hari ranar Lahadi a yankin Okeluse da ke Ƙaramar Hukumar Ose ta Jihar Ondo.
Jaridar TheCable ta ce an kai harin ne da misalin karfe 9:00 na dare ranarLahadi.
Aborowa Oladimeji, manajan wani gidan mai da ke cikin garin ya rasa ransa a harin da aka kai.
An saka wani bidiyo da ke nuna gawarsa a shafin zumunta na Facebook.
‘Yan bindigar sun kashe É—aya daga cikin ma'aikacinsa wanda ba a bayyana sunansa ba.
Wani mutum da ya shaida afkuwar lamarin ya ce "makiyayan sun harbi wani ma’aikacin gidan man. An yi gaggawar kai shi asibiti amma bai rayu ba".
"Manajan gidan mai É—in ya rasu nan take kuma makiyayan sun zo ne a lokacin da yake kokarin barin gidan man tare da yaron nasa".
Harin ya faru ne ‘yan makonni kaÉ—an bayan mutum biyar sun rasa rayukansu a garin Arimogija a karamar hukumar ta Ose.
No comments