Barayin daji sun sace sama da mutum 50 daga kauyen Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a arewa maso gaba...
Barayin daji sun sace sama da mutum 50 daga kauyen Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a arewa maso gabashin Najeriya.
Jaridar DailyTrust ta kasar ta ruwaito cewa, wani dan yankin wanda ya nemi a boye sunansa ya sheda mata cewa maharan su sama da 60 sun je ne a kan babura inda suka bude wuta, suna harbin kan mai-uwa-da-wabi.
Ya ce ‘yan bindigar sun ci karensu ba babbaka tsawon sa’a biyu, ba tare da wasu jami’an tsaro sun kai dauki ba, duk da cewa akwai sojoji kusan 20 a kauyen, in ji jaridar.
Mutumin ya kara bayani da cewa, tun ma kafin mutanen su je garin sun samu bayani a kan shirin zuwan, kuma sun gaya wa jami’an tsaro, amma abin takaicin maharan sun je da kusan karfe 7:30 na al’muru, inda suka shafe sa’a biyu a garin.
‘’Sun raunata mutum uku amma ba su kashe kowa ba, sai dai kuma sun sace sama da mutum 50 bayan kwashe wasu kayayyaki da suka hada da tufafi,’’ in ji mutumin.
Wanei dan garin ya yi zargin cewa sojoji da suka fito daga bangaren garin Sheme na karamar hukumar sun ga maharan suna tsallaka titi da mutanen da suka sace, amma kuma ba su yi wani yunkuri na cetarsu ba.
No comments