RFI ta labarto cewa; Igor Bogdanoff, daya daga cikin tagwayen nan da suka shahara a wani shrin gidan talabijen na Faransa TF1 ya...
RFI ta labarto cewa; Igor Bogdanoff, daya daga cikin tagwayen nan da suka shahara a wani shrin gidan talabijen na Faransa TF1 ya rasu jiya litinin a birnin Paris ya na mai shekaru 72, rasuwar sa na zuwa kusan kwanaki shida bayan rasuwar Grichka Bogdanoff dan uwan sa.
An dai bayyana cewa sun mutu ne bayan kamuwa da kwayar cutar covid 19,sai dai kafin rasuwar su sun samu kulawa da ta dace daga jami’an kiwon lafiya.
Lauyan 'yan tagwayen mai suna Édouard de Lamaze ya shaidawa manema labarai cewa sun mutu ne bayan kamuwa da cutar korona.
Tun daga ranar 15 ga watan Disambar 2021 ne aka kwantar da su asibitin Georges Pompidou bayan gano cewa sun kamu da kwayar cutar Covid 19, tagwayen da suka hada da Igor Bogdanoff da Grichka sun ki karbar allurar rigakafin cutar korona.
No comments