Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Za Mu Yi Wa Dan Majalisarmu Isa Hazo Kiranye, Cewar Isma'il Kafinta Basawa

Aisha Suleiman, Zariya A ci gaba da jin ra'ayoyin jama'a akan moriyar da suka samu a karkashin dimokuradiyya a lokacin b...


Aisha Suleiman, Zariya

A ci gaba da jin ra'ayoyin jama'a akan moriyar da suka samu a karkashin dimokuradiyya a lokacin baya da kuma yanzu musamman a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Wakiliyarmu ta sami zuwa garin Basawa don jin ta bakin mazauna garin a wannan lokacin.

Isma'il kafinta na daya daga cikin matasan garin Basawa kuma fitacce a cikin garin wanda matasa ke amsa masa a duk lokacin da ya koka  bangarori da dama.

A zantawarsa da Jaridar Madogara a tsakiyar garin na Basawa kuma a birnin Jama'a, matashin ya yi ikirarin  tabbatar da kiranye ga dan majalisarsu na jiha mai wakiltar mazabarsu wato Honorabul Muntari Isa Hazo.

Isma'il Kafinta ya yi koka matuka game da halin da jama'ar yankin suka shiga game da halin ko in kula da dan majalisar na su ya nuna masu a siyasance.

Ya ce a halin yanzu babu wani abu da za su ce wa Honorabul Muntari Isa Hazo sai maganar kiranye da za su yi masa nan bada jimawa ba don Hausawa suna cewa laifin yaro kyuya lafin babba rowa.

Isma'il Kafinta ya bayar da misali irin halin da garin ya tsunduma ta rashin hanya da magudanan ruwa ya kawo misali da wata hanya da ta taso daga tashar Rahama ta nufi Anguwar Madaki ta nufi Kofar Fada  ya ce yanzu haka ruwa ya zaizaye hanyar duk da tasirin da hanyar ta bayar lokacin neman kuri'un talakawan yankin.

Bisa haka ne ya ce a lalin yanzu babu wani aikin ci gaba da wani zai nuna ya ce Honorabul Isa Hazo ne ya kawo shi a siyasance. Tuni matashin ya yi kira ga ilahirin jama'ar yankin Basawa da su yi hakuri su barwa Allah komai ranarsu tana nan tafe.

Da ya juya kan dan majalisar kuwa ya roke shi ne da babban murya cewa ya tuna amanar dake kansa wanda Allah na iya tambayarsa a ranar alkiyama.

A ƙarshe matashin ya yi fatan Allah yasa dan majalisar ya ji tsoron Allah ya dubi nauyin da ya hau kansa na bai wa jama'ar da yake wakilta gudummawa ta kowanni fanni.

Yayi rokon Allah ya kawo masu dauki akan halin rashin ci gaban yankin da gaggawa.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa a cikin garin cewa ya yi maganar rashin aiki da ake magana a kai gaskiya ne, ya ce, amma ai ba dan majalisar ke yin aikin ba shima rubutawa zai yi ya aikawa na gaba da shi in sun tabbatar sai a zo a duba in ya dace sai a gabatar da aikin ya ce don haka ba laifin dan majalisar bane don haka a yi addu'a kawai Allah ya zaba masu shugabanni na gari.

Bincike ya nuna cewa garin Basawa na daya daga cikin yankin dake da ruwan kuri'u a cikin mazabun da ke a karamar hukumar ta Sabon Gari.

Bugu da kari garin ya shahara wajen fitattun 'yan siyasa da gogewa a siyasa wato sun san kabli da ba'adinta kuma sun san hagu da dama.

Ya zuwa yanzu jama'a dama sun ja bakinsu sun rufe amma suna da nufin amfani da kuri'unsu don zabar wanda zai masu aiki tukuru ga yadda binciken ya nuna a zahiri.

No comments