Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaben 2023: Matasan Jigawa Sun Bukaci Ahmed Gumel Ya Amsa Kiransu Na Tsayawa Takara

Daga Abubakar M. Taheer Wasu matasa masu fafutukar kawo chanji a siyasar jihar Jigawa sun miko ƙoƙon barar su ga tsohon mataimak...


Daga Abubakar M. Taheer

Wasu matasa masu fafutukar kawo chanji a siyasar jihar Jigawa sun miko ƙoƙon barar su ga tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Ahmed Mahmud Gumel kan ya fito takarar gwamnan jihar Jigawa a zaben 2023 mai zuwa.

A matsayinmu na matasa masu fatan ci gaban jiharmu abar alfaharinmu muna bukatar a ce jihar mu ta Jigawa ta zama cikin fitattun jihohin da ake alfahari da su a Nijeriya. Sakamakon duba da kuma hangen cancanta tasa muka bukaci Alhaji Ahmed Mahmud Gumel ya zamanto gwamnan", inji su.

Sun ci gaba da cewa; "Da farko Hon. Ahmed Mahmud Gumel tsohon dan siyasa ne wanda ya fara siyasa tun a shekarar 1978 kusan shekaru 44 ke nan a yanzu don haka hannunsa ya dade da fadawa a siyasa yama zama Ubangida.

"Na biyu Hon. Ahmed ya rike Ciyaman na Jam'iyyar SDP a lokacin da Alhaji Ali Sa'adu Birnin Kudu yake gwamnan Jigawa a shekarar, sannan kuma ya zama 'Returning Officer' a zaben cikin gida A lokacin Mulkin Marigayi Sani Abacha da Marigayi MD Yusuf a UNCP da DPM.

"Alhaji Ahmed Mahmud Gumel ya zama mai bawa tsohon  gwamnan jihar Jigawa Alhaji Saminu Ibrahim Turaki Shawara kan gidaje da Safiyo daga baya Gwamna Saminu ya duba kwazonsa ya maida shi mai bashi shawara kan kula da gyare-gyaren titunan jihar Jigawa, da kuma mai bashi shawara kan 'Formal' da 'informal education'.

"Daga nan Ahmed Mahmud Gumel ya samu ci gaba inda aka bashi Kwamishina dake kula harkokin gwamnati.

"Daga nan Ahmed Mahmud ya zamanto jami'a mai kula da hulɗa tsakanin hukumomin gwamnati, sakamakon ganin irin kwazonsa da ayyukan ci gaban al'umma.

"Ahmed ya sake samun damar zama Kwamishinan kudi da tsara tattalin arziki a gwamnatin Saminu Ibrahim Turaki kuma lalle kwalliya ta biyan kudin sabulu.

"Bayan da tsohon gwamnan jihar Saminu Ibrahim Turaki ya gama mulkinsa, anyi duba da wanda ya cancanta wannan tasa  Gwamna Sule Lamido ya bashi takarar mataimakinsa suka sami nasarar cin mulki a shekarar.

"Hon. Ahmed Mahmud ya sami damar kasancewa Kwamishinan Rabon tattalin arziki na kasa, wato hukumar FISCAL.

"Ya kuma sake zama daya daga cikin masu gudanar da hukumar rabon tattalin arziki kasa wato 'National Salary Income and Wages Commission'.

"Hon. Ahmed Mahmud ya saka Darakta janar na kula da yakin zaben gwamna Muhammadu Badaru wanda aka kai ga cimma nasara a zaben 2015 dana 2019.

"Da Wadannan cancanta ta mai girma Ahmed Mahmud Gumel muke ga ya dace ya karbi wannan bukata tamu domin sake fito da jiharmu abar alfarinmu a idon duniya baki daya", suka lurantar.

No comments