Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta tsare manajan darektan kamfanin sufurin jirgin sama na ...
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta tsare manajan darektan kamfanin sufurin jirgin sama na Medview Airline, Alhaji Muneer Bankole a kan zargin cin kudin aikin hajji.
Hukumar ta zarge shi da karkatar da kashi 50 cikin dari na kudaden da hukumar aikin hajji ta Najeriya ta biya shi da kuma wasu karin dala dubu 900 domin jigilar alhazai a 2019, aikin da bai yi ba.
Rahotanni sun ce EFCC ta tsare shi ne Litinin din nan da rana a babban ofishin hukumar da ke unguwar Jabi a Abuja.
Rahotannin sun kara bayani da cewa Alhaji Muneer, ya amsa gayyatar hukumar ne inda ya je hedikwatar tata da misalin karfe 11 na safe, domin amsa tambayoyi kan kin aikin jigilar bayan ya karbi wadannan kudade na soma aiki.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da tsare shugaban inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
No comments