Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Nijeriya wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) a turance, ta ce tana neman ɗan sanda DC...
Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Nijeriya
wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) a turance, ta ce tana neman ɗan sanda DCP
Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Wata
sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce bincikensu ya nuna cewa Abba
Kyari na cikin wata ƙungiya da ke safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen Brazil da
Ethiopia zuwa Najeriya.
Idan ba
a manta ba, a watan Yulin 2021 ne rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta dakatar da
DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan 'yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci
daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid - mutumin da ke tsare a
Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.
Ta ƙara
da cewa jami'an NDLEA sun gayyaci ɗan sandan don ya amsa tambayoyi game da
zarge-zarge amma ya ƙi zuwa, "abin da ya sa muka yi wannan taron manema
labaran kenan"
No comments