Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC a Nijeriya da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ke jagoranta ya gabatar da wasu shawar...
Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC a Nijeriya da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ke jagoranta ya gabatar da wasu shawarwari da yake sa ran za su zama mafita ga rikicin jam'iyyar ta su a jihar Kano.
A jiya ranar Asabar ne kwamitin rikon ya yi wani kiran tattaunawar gaggawa tsakanin bangaroroin biyu, bayan tattara bayanan da ya yi a ranar Talatar 25 ga watan Janairun da ya gabata.
Dr Sule Ya'u Sule shi ne mai magana da yawun Sanata IbrahimShekarau, ya bayyana cewa an cimma wani bangare na matsaya amma akwai sauran bayanai da za a samu a ranar Litinin daga Kwamitin.
"Cikin abubuwan da aka gabatar wa bangarorin biyu akwai batun cewa jam'iyya ba ta bangare daya ba ce, kuma ko wanne bangare dole ya tafi da dan uwansa, domin samun nasara da ciyar da jam'iyyar gaba," in ji Malam Sule.
Amma za a gabatar da cikakkun shawarwarin a ranar Litinin, kuma ana sa ran duka bangarorin biyu za su mika wuya ga wannan yarjejeniya wadda za ta samar da mafita a jihar.
Hon Kabiru Alhasan Rurum tsohon shugaban Majalisar jihar Kano ne, kuma yana tare da gwamna Ganduje, ya ce "Muna da kyakkyawan zaton wannan lamar yazo karshe domin, uwa daya muke uba daya muke.
"Abin da muke zaton ji maslaha daga kwamitin riko na wannan jam’iyya, saboda duka bangarorin mun yi wa juna wahala a baya," in ji Alhasn Rurum.
Daga baya ana sa ranar bayyana wanda zai zama shugaban wannan jam'iyya ta APC mai mulki a jihar ta Kano.
A makon da ya gabata ne, yayin wani gagarumin taro aka bai wa shugabannin jam'iyyar APC a mataki na jihar shaidar zama halastattun shugabannin jami'iyya amma ba a bai wa jihar Kano da Sokoto ba saboda rikicin da ake fama da shi.
Cikin wadanda suka halarci wannan zama akwai gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da Sanata Malam Ibrahim Shekarau, da Sha'aban Sharada da Kabiru Gaya da dai sauransu.
-Rahoton BBC
No comments