Daga Ali Kakaki A 'yan kwanakin nan, a duniyar yanar gizo-gizo ba a samu abin da ya tada hazo ba, sama da rikicin da ya shig...
Daga Ali Kakaki
A 'yan kwanakin nan, a duniyar yanar gizo-gizo ba a samu abin da ya tada hazo ba, sama da rikicin da ya shigo masana'antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood, tun bayan sakin hirar Ladin Cima, wanda mutane suka fi sanin ta da Baba Tambaya wacce ta yi da kafar sadarwa ta BBC Hausa.
Tun ranar da BBC Hausa suka saki rahotan nake kokarin harhada hujjoji daga dukkan bangare guda biyu, bangaren Ladin Cima da kuma abokan sana'arta. Abin da na fahimta shi ne, tabbas shaidan ya taka muhimmiyar rawa a bangarorin biyu duba da yadda maganar ba ta kai ta kawo ba, wacce za a iya sulhunta ta, a samo mafita cikin abin da bai wuce awa daya ba idan aka zauna aka fahimci juna, mai kuskure a ba shi kuskurensa, sannan a yafi juna a kuma ci gaba da mu'amala da juna cikin girmamawa.
A lokacin da na tuntubi Ladin Cima a waya, mun yi magana cikin fahimta, kuma cikin alhini take bayyana min cewa yanzu haka ma tana cikin damuwar rashi har guda biyu da suka same ta kasa da wata uku da suka wuce, na farko mahaifinta Allah ya mishi rasuwa sai kuma babban danta shima Allah ya karbi ransa cikin abin da bai wuce kwana goma sha biyar ba da suka wuce, ga kula da yara sama da biyar da suke karkashinta, ga kuma shekaru da suka ja.
Tabbas ko iya wadannan abubuwa aka duba, aka dauki daya daga cikinsu ya kamata a daraja Ladin Cima a barta haka nan, duk maganar da ta furta a mata uzuri akan ta.
Shi fa dan halak ko ya ya yake baya manta halacci, wannan maganar Ladin Cima ta bayyana mun, kuma tana sane da dukkan halaccin da 'yan fim suka mata, kuma a kowanne lokaci tana musu fatan alkhairi kamar yadda ta bayyana mun.
A shawarce a ganina, a irin wannan lokaci babu abin da Baba Tambaya take bukata duba da girman shekarun ta irin kwanciyar hankali, kuma idan har ba mu zama silar kwantar mata da hankali ba, bai kamata mu zama silar tayar mata da shi ba.
Da yawan matasan Æ´an fim din nan, Ladin Cima ta fara fim tun kafin ma a haifi iyayensu, tunda fiye da shekaru hamsin baya ma ana dora mata kyamara, saboda haka, ko baka girmama ta ba don shekaru yakamata ka girmamata domin ta shuka alkhairin da a yau shi ne ya yi maka riga da wando.
A karshe zan yi tunatarwa da kuma bada shawara ne ga abokan sana'ar Ladin Cima, da farko ku sani cewa babu wata masana'anta kowacce iri ce da za ta yi albarka matukar yaran cikinta ba sa girmamawa da daraja Dattijan cikinta, ku binciki dukkan wata masana'anta dake duniya, wadanda suka samar da ita sune ginshikanta wadda taba su tamkar karya lagon kune, dole a kula da wannan a kiyaye idan ana son ganin daidai.
Na biyu; a ganina a shawarce mai zai hana mu tausayawa wannan baiwar Allah, ba domin muna raina abin da ake ba ta ba, a'a sai domin nuna godiya ga irin gudummawar da ta bayar wajen kafuwar wannan masana'anta tun daga jaririyar ta mu taimaka mata da dukkan abin da muke ganin zamu iya bayarwa na tallafi a gareta na abin da ya samu.
No comments